3 Agusta 2020 - 13:45
Jami’an Tsaron Hadin Guiwa Na Iraqi Za Su Samar Da Sabon Shirin Yaki Da Daesh

Gamayyar jami’an tsaron kasar Iraqi za su fidda wani sabon shiri na yaki da ragowar mayakan kungiyar ‘yan ta’adda ta daesh a kasar.

ABNA: Tahsin Khaffaji kakakin gamayyar jami’an tsaron ya fadawa kamfanin dillancin labaran “Waa” na kasar ta Iraqi kan cewa, ragowar mayakan kungiyar Daesh su na shirin kaddamar da hare-hare a kasar a dai-dai lokacinda kasar ta ke fama da tsananin ra na da kuma yaduwar annobar cutar Korona.

Khaffaji ya kara da cewa a halin yanzu jami’an tsaron kasar sun samar da maduban hangen nesa na musamman don ayyukan rani, wadanda zasu taimaka wajen gano kai kawon ‘yan ta’adda a duk fadin kasar. Ya kuma kara da cewa za su yi amfani da jiragen leken asiri don karfafa ayyukan tsaro a duk fadin kasar.

Tun cikin watan Nuwamban shekara ta 2017 ne dai, aka kawo karshen ikon kungiyar ‘yan ta’adda ta Daesh a kasar Iraqi, amma har yanzun akwai daddaikunsu a boye a wurare da dama a kasar.

342/